Majalisar wakilai ta ba cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC tabbacin samar da kudade da za a rika amfani dasu wajen inganta dakunan gwaje-gwajen cutar korona dake fadin Najeriya.
Kwamitin yaki da cutar na majalisar ya bayyana haka a lokacin da ‘yan kwamitin tare da rakiyar shugaban cibiyar ta NCDC suka kai ziyara cibiyar gwajin dake Kaduwa a Abuja.
Shugaban kwamitin Haruna Mshelia, ya ce za a inganta dukkanin cibiyoyin gwaje-gwajen cutar dake fadin Najeriya da wadatattun kayayyaki.
Sannan ya bada tabbacin cewa kwamitin zai ci gaba da bada cikakken goyon baya dan ganin an samu inganci a gwaje-gwajen cutar da ake gudanarwa a fadin kasar nan.
A nasa bangaren shugaban cibiyar ta NCDC ya bukaci a ci gaba da maida hankali wajen inganta bangaren lafiya a Najeriya ko bayan yakar cutar korona.
Ya kara da cewa dakin gwaje-gwaje na kasa da aka samar a shekarar 2018 ya aje samfri na wadanda aka gwada ko suna dauke da cutar korona ko babu guda dubu 40.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *