Atoni Janar ta tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce har yanzu ofishinsa bai karbi dala billiyan 62 na hadakar kamfanonin kasashe na man fetur ba.
Malami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Umar Gwandu.
Malami ya ce wasu rahotanni dake yawo a wasu kafofin yada labarai na karbar kudaden ba gaskiya bane.
Ya ce ma’aikatar a shekara guda da ta gabata ta bayyana irin kokarin da take na karbo kudade da kokarin da take na ganin kudaden basu dilmiya ba a kamfanonin na kasashen katere.
Ko a ranar Talatar da ta gabata ministan a lokacin da yake jawabi a wajen taron bitan da aka shiryawa manema labarai a bangaren shari’a, ya bayyana kudadee da ma’aikatar ta karbo.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *