Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da bunkasa harkokin sadarwa na zamani domin cimma muradin tabbatar da gudanar da gwamnati ta fasahar, tare da bunkasa tattalin arziki bayan kawar da cutar korona.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manyan jami’an cibiyar kula da harkokin sadarwa na zamani a Abuja.
Mustapha ya ce cibiyar ta kasance abin dogaro wajen gudanar da harkokin gwamnati, musamman a yanzu da cutar korona ta tsaida bangarori da dama.
Da yake jawabi shugaban cibiyar Muhammad Abubakar, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa irin goyon baya da yadda da ta nuna ga bangaren.
Abubakar ya ce cibiyar za ta ci gaba da aiki da gwamnatoci da dukkanin matakai wajen tabbatar anyi amfani da damar da ake da ita a bangaren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *