Gwamnatin tarayya ta ce ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen magance durkushewar tattalin arzikin kasa bayan kawar da cutar korona a Najeriya, kamar yadda wasu cibiyoyin kasashen duniya ke hasashe.
Ministan kula da harkokin zuba jari da masana’antu, Adeniyi Adebayo ya bada tabbacin a Abuja, a lokaicn da yake bada lambar yabo ga ‘yan kwamitin daukar matakin gaggawa wajen kai kayayyaki sassa daban-daban a wannan lokaci na yaki da cutar korona.
Adebayo ya ce gwamnatin tarayya na da kudurin ba bangarorin samarwa tare da sarrafa kayayyaki da sauran bangarorin bunkasa tattalin arziki tallafi na musamman.
Ministan ya kuma yabawa kwamitin na irin kokarin da ya yi wajen sauke nauyin dake kansa, ya kara da cewa bisa la’akari da shawarwari da gwamnati ta samu, Najeriya za ta iya samar da wasu kayyakin amfanin yau da kullum da ake bukata.
Ita ma karamar minister kula da harkokin kasuwanci da zuba jari, Maryam Katagum, ta ce cutar korona ta barwa ‘yan Najeriya darasin cewa duka za su iya bada gudunmawa wajen bunkasa tattalin arziki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *