Wasu ‘yan ta’adda sun kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum hari a garin Baga.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta ce ‘yan ta’ addan sun kaiwa gwamnan harin ne a lokacin da yake kan hanyar kai ziyarta sansanonin ‘yan gudun hijira dake yankin.

Majiyar ta ce gwamnan ya kammala ziyara a sansanin Kukawa, inda ya nufi Baga kafin ‘yan ta’addan suka kai harin.

Majiyar ta kara da cewa ba wanda ya samu rauni a harin.

Sai dai har yanzu babu tabbaci na kungiyar ta’addancin da ta kai harin, amma kungiyar Boko Haram ce ke kai hare-hare a yankin na Arewa maso gabas.

Wannan dai shine karo na biyu da ake kaiwa tawagar gwamnan hari a wannan shekarar, domin ko a kwanakin baya ‘yan ta’addan sun kai wa ayarain motocinsa hari a lokacin da yake komawa Maiduguri daga Bama.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *