Gwamnatin tarayya ta ce nan gaba kadan za ta karbi dala miliyan 200 daga cikin badakalar cinikin rijiyar mai na Malabu daga kasashen Netherland da Switzerland.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana haka a Abuja, ya ce an samu nasarar ce sakamakon yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.

Ya ce Najeriya ta yi nasarar kwato kudin da ya kai dala biliyan 62 daga hannayen kamfanonin mai.

Ya ce har ila yau gwamnatin tarayya ta karbo dala miliyan 311 daga gwamnatin Amurka da New Jersey daga cikin kudaden da Abacha ya aje a kasashen ketare, da kuma wasu karin dala miliyan 6 da dubu dari 3 daga kasar Ireland.

Ministan Shari’ar ya ce, gwamnatin tarayya ta yi nasarar kwato Naira miliyan 685 a cikin shekara guda da taimakon masu masu tauna asirin almundahana, yayin da gwamnati ta kuma samo naira miliyan dari 5 daga jiragen ruwa da tankunan mai da ake amfani da su wajen sace man fetur.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *