Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an sake samun karin mutane  624 da suka kamu da cutar korona a jihohi 21 ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafin ta na twitter, ta ce yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar tun bayan bullar ta a watan Fabrairu sun kai dubu 41 da 804.

NCDC ta ce, an kuma sake samun mutane 8 da suka rasa rayukansu cikin sa’o’i 24, wanda yanzu adadin wadanda suka mutu tun bayan ɓullar cutar a Nijeriya ya kai 868.

Alƙaluman cibiyar sun nuna cewa masu korona 18,764 ne suka warke tun bayyanar cutar a ƙasar.

Har yanzu Lagos ce jihar da ta fi fama da cutar a Najeriya, inda aka sake gano masu korona 212 a ranar Talata.

A birnin Abuja da ke zama na biyu a yawan masu fama da cutar a Najeriya, masu cutar korona 35 aka gano.

A jihar Kaduna, an sake gano mutum huɗu sai da suka kamu da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *