Majalisar dattawa ta gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad, da ministan kula da ayyuka sa damar da gidaje Babatunde Fashola domin su yi bayani kan kudaden wasu manyan ayyuka 3 da gwamnatin tarayya ta gada.

Har ila yau majalisar ta gayyaci Akanta janar na tarayya Ahmad Idris, da shugaban hukumar kula da harkokin zuba jari a bangaren ayyuka Uche Orji.

Majalisar ta gayyaci mutanen ne a wajen wata ganawa da kwamitin dake kula da harkokin kudade ya yi da jami’an hukumar hukumar kula da harkokin zuba jari a bangaren ayyuka.

Ayyukan dai sun hada da babbar hanyar Abuja zuwa Kano, da Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Niger na 2.

Asusun kula da aikace-aikacen ci gaban kasa na shugaban kasa ne ya fitar da kudaden da za a gudanar da ayyukan.

Shugaban kwamitin majalisar Solomon Olamilekan, ya ce an gayyaci shugabannin hukumomin da na ma’aikatun ne domin yin bayani kan wasu bambance-bambance da ake samu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *