Gwamnatin jihar Yobe ta kaddamar da aikin dashen bishiyoyi miliyan 3 a fadin jihar.

Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya jagoranci bikin kaddamar da dashen bishiyoyin a Damaturu babban birnin jihar.

An kaddamar da shirin ne karkashin ma’aikatar muhalli bisa jagorancin kwamishinan ma’aikatar Sidi Yakubu Karasuwa.

Ma’aikatar ta ce ta samar da bishiyoyin ne dan gudun gurbatar yanayi da kaucewa hamada da kuma zaftarewar kasa a fadin jahar.

Jahar Yobe dai na makwaftaka da jamhuriyar Niger inda tayi iyaka da kananan hukumomin Yunusari, Geidam Yusufari, Machina da Karasuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *