Gwamnatin tarayya ta kara kwaso ‘yan Najeriya 289 da suka makale a kasar Amurka sakamakon matakin da gwamnatoci suka dauka na rufe kan iyakokin kasa domin dakile yaduwar cutar korona.

Jakadan Najeriya a birnin New York Benaoyagha Okoyen ne ya tabbatar da haka ya ce wannan shine jigila na hudu da ya kawo adadin yawan mutanen da aka kwaso daga kasar ta Amurka zuwa dubu 1 da 95. 

Jirgin sama kasar Habasha ne ya kwaso mutanen a jiya Talata kuma ake kyautata zaton zai sauka yau da ranan nan a babban birnin tarayya Abuja.

Okoyen ya ce an bar wasu mutane da dama ciki har da wasu ‘yan uwa su 7 sakamakon rashin nuna sakamakon gwajin da aka musu na cutar korona, wanda na daya daga cikin sharuddan dawo da mutanen.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta amince da karin maido da wasu ‘yan Najeriya dake biranen Texas da New Jersey, a ranar 31 ga watan nan da kuma 7 ga watan Agusta mai zuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *