Ministan kula da ayyuka da samar da gidaje Babatunde Fashola, ya ce ma’aikatarsa ta tura da kwararru kan kimiyya da fasaha domin su yi nazari tare da gano musabbabin yawan haddura da ake samu a gadar Kara dake Legas.

Gadar ta Kara dai dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan ta kasance waje mai hadarin gaske da ake yawan samun haduran ababen hawa musamman motoci, tare da rasa rayuka da dukiyoyi.

Fashola ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ziyarar gani da ido kan irin halin da hanyoyin ke ciki da kuma irin cunkoson ababen hawa da ake samu tun bayan sassauta dokar takaita zirga-zirga.

Ya ce ana sa ran kwararrun da aka tura za su yi bincike tare da gano dalilan da ke sa ana samun karin aukuwar haddura a gadar da kewaye.

Sai dai ya zargi direbobin mota musamman ma na manyan motoci da yin ganganci a duk lokacin da suke kan hanya, wanda a cewarsa hakan na kawo hadari sosai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *