Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin Sabi’u Abubakar da Oba Olaniyi, a matsayin sabbin mataimakan kwamishina a Hukumar Inshora ta Najeriya NAICOM.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da babban kwamishinan NAICOM Rasaaq Salaami,  ya fitar yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

Salami ya ce Abubakar zai kasance mataimakin kwamishina mai kula da tsare-tsare a hukumar yayin da Oluniyi zai kasance mataimakin kwamishina mai kula da harkokin gudanarwa.

Sanarwa ta ce nadin ya fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yuli za kuma su kasance a kan mukamin har zuwa shekaru 5 masu zuwa.

Sanarwar ta kuma yi bayanin cewa, za a fara lissafin tasirin naɗin mukamin tun daga ranar 17 ga watan Yuli, har zuwa nan da shekaru biyar masu zuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *