Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an salami mutane dari 8 da 29 da aka tabbatar sun warke daga cutar korona a cibiyoyin kula da masu dauke da cutar dake fadin Najeriya.

Cibiyar wacce ta bayyana haka a shafin ta na twitter, ta ce wannan shine karon farko da aka samu mutane masu yawan haka da suka warke daga cutar tun bayan bullar ta a watan Fabrairun wannan shekarar.

Ta ce tun bayan bullar cutar zuwa yanzu, mutane dubu 18 da dari 2 da 3 ne aka tabbatar da sun warke, kuma an sallame su daga cibiyoyin kula da masu dauke da cutar.

Cibiyar ta kara da cewa an samu karin mutane dari 6 da 48 da suka sake kamuwa da cutar a jihohi 21 dake fadin kasar nan, wanda yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullar ta ya kai dubu 41 da dari da 80.

Sai dai cibiyar ta ce mutane 2 sun sake rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *