Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta ce runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso yamma ta kama tare da kashe wasu ‘yan ta’adda da suka shahara wajen garkuwa da mutane, satar shanu, da sauran ayyukan ta’addanci a yankin.

Mai rikon mukamin jami’in yada labarai na shelkwatar Birgadiya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Onyeuko, ya ce ko a ranar 22 ga watan nan jami’an sojin sun kama kasurgumin dan ta’adda mai suna Musa Abubakar da aka fi sani da Kasko-Buzu, dan asalin kauyen Mai Wake dake jamhuriyar Nijar.

Ya ce an kama mutumin ne a harabar wata makatanta dake Gusau a jihar Zamfara inda wani dan uwanshi ke aiki a matsayin mai gadi.

A cewarsa wanda aka kaman na daga cikin masu safarar makamai daga jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya ta kan iyakar kananan hukumomin Sabon Birni da Isah dake jihar Sokoto.

Har ila yau Onyeuko ya ce a ranar 25 ga wannan watan ma jami’an sojin sun kashe ‘yan ta’adda biyu a Gurbin Baure.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *