Gwamnatin tarayya ta gana da shugabannin kungiyar likitoci ta Najeriya akan barazanar da kungiyar ta ke na tsunduma cikin yajin aiki sakamakon rashin biya musu bukatun su.

An kammala ganawar da ta gudana a Abuja ne da kyautata zaton kungiyar za ta janye yajin aikin.

Ministan kwad0ago da samar da ayyukan yi Chris Ngige, wanda ya jagoranci ganawar ya ba likitocin tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta duba korafe-korafen da suke da shi.  

Wannan na zuwa ne bayan likitocin sun ba gwamnatin tarayya wa’adin makwanni 3 na su biya musu bukatun su ko su tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.

Bukatun da likitocin suka gabatar sun hada da kula da jin dadin su, shirya musu horo na musamman kan makaman aiki, da kuma inganta cibiyoyin kula da lafiya da asibitocin gwamnati.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *