Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 30 ga watan Yuli da Juma’a 31 ga wannan watan a matsayin hutun babbar Sallah na shekarar 1441 bayan hijira.

Ministan kula da harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren ma’aikatar Georgina Ehuriah, a Abuja.

Ministan ya taya al’ummomin Najeriya na gida da kasashen ketare musamman Musulmai murnar zagayowar wannan lokaci na Sallah.

Sannan ya bukaci al’ummomin Musulmai su rungumi dabi’ar son zaman lafiya da kaunar juna, ta hanyar yin koyi da manzon Allah Sallalahu Alaihi Wa Sallam.

Ministan ya bukaci al’ummar Musulmai su yi amfani da wannan lokaci mai muhimmanci wajen yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya, daidaito da ci gaba da yakar cutar korona.

Aregbosola ya bada tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana wajen samun hadin kai da daidaito a tsakanin ‘yan Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *