Gwamnatin tarayya ta ce an yiwa mutane dubu dari 2 da 62 da dari 5 da 79 gwajin cutar korona a cikin watanni biyar da suka gabata.

Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya tabbatar da haka a lokacin da yake jawabi a taron kwana-kwana karo na 53 da kwamitin yaki da cutar korona wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa ke shiryawa a Abuja.

Ya ce duk da cewa yawan wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullar ta a Najeriya ya haura dubu 40, mutane dubu 17 da dari 3 da 74 ne suka warke daga cutar. 

Ministan ya kara da cewa yanzu haka akwai cibiyoyin gwajin masu dauke da cutar 60 a fadin Najeriya na kwamitin yaki da cutar wanda shugaban kasa ya kafa.

Ya ce kadan ne daga cikin masu ciwon siga, ciwon hanta, asma, suka rasa rayukansu bayan sun kamu da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *