Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wasu aikace-aikace da shirye-shiryen da za su taimaka wajen farfado da tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani wanda hukumar kula da harkokin sadarwa na zamani ta samar.

Shirin wanda ministan kula da harkokin sadarwa da fasahar zamani Isa Ali Pantami, ya kaddamar sun hada da wanda aka samar a jami’ar  Ahmadu Bello dake Zaria, da Jami’ar Legas, da kuma cibiyar fasahar zamanin da aka samar a garin Daura dake jihar Katsina.

Pantami ya ce tsarin ya shafi bangarori 3 na bunkasa tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.

Ya ce cibiyoyin fasahar zamani da aka samar a Kaduna da Legas za su maida hankali wajen ci gaban fasahar zamani tare da saukakawa wadanda ke da fasahar ta yadda za su bada gudunmawa da kuma tsayuwa da kafafun su.

Sauran wadanda suka halarci taron kaddamarwar sun hada da minister kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad, Ministan Ayyuka da samar da gidaje, Babatunde Fashola, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *