Tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya ce bada kwangiloli ba bisa ka’ida ba da gwamnatin jihar Bauchi ke yi, ya na daga cikin manyan dalilan da su ka sa shi watsar da shahadar jam’iyyar PDP ya koma APC.

Dogara, ya kuma bayyana damuwa a kan rashin biyan ma’aikata albashi a kan lokaci, da kuma rashin gudanar da zabubbukan kananan hukumomi cikin watanni shida na farko kamar yadda gwamna Bala Muhammad ya yi alkawarin zai yi.

Ya ce gwamnati ta ciyo bashin Naira biliyan hudu, daga baya aka gano kudin a asusun wani kamfani mai zaman kan sa, duk da cewa an ranto su ne da sunan jihar Bauchi, sannan ana bada kwangiloli ba bisa ka’ida ba, baya ga ninka kudin da ake yi yadda aka ga dama ba tare da bin ka’idojin doka ba.

Yakubu Dogara ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun sa Turaki Hassan, inda ya ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda hankoron samun wata dama a jam’iyyar APC.

Ya ce wata matsalar da ya gani a shugabancin gwamnatin PDP a jihar Bauchi ita ce, rashin girmama manya da sarakuna da gwamnan ke yi, saɓanin alkawuran da ya yi a baya cewa zai rika daraja su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *