Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da sabuwar dokar kula da tsarin tafiyar da harkokin kudaden gwamnatin jihar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta rage kasafin ta na bana da kimanin naira biliyan 70 saboda mummunan tasirin da annobar korona ta yi ga tattalin arzikin jihar,

Sai dai kungiyoyin rajin shugabanci nagari na cewa, batun samar da doka lamari ne mai sauki, amma aiwatar da shi shi ne kalubale.

Samar da sabuwar alkiblar tafiyar da kudaden gwamnati bisa tsarin dimokaradiyya dai na daga cikin manufar sabuwar dokar a jihar Kano, wadda tun a shekarun baya aka samar da ita a matakin tarayya da ma wasu jihohin Nijeriya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ta jihar Kano Kabiru Hassan Dashi ya shaida wa manema labarai cewa, dokar za ta ba ma’aikatu da gwamnatin jihar ka’idar yadda za su kashe kudaden su, tare da yadda jihar za ta kasafta kudin ta.

Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci nagari sun yi maraba da wannan doka, muddin dai za a bi ta sau da kafa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *