Gwamnatin Tarayya ta tsawaita lokacin da za ta rufe karbar rajistar rukuni na uku na masu neman aikin shirin N-Power har zuwa tsawon makonni biyu.

Shigar da rajistar neman aikin N-Power ta hanyar yanar gizo, an fara ta ne tun daga ranar 26 ga watan Yuni na shekara ta 2020, aka kuma kayyade za a rufe a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli.

Gwamnatin ta sanar da cewa, ta kara tsawon makonni biyu ne don a ba matasa damar shigar da bukatun neman aiki a shiri na tallafa wa wadanda su ka kammala karatu kuma ba su da aikin yi.

Ta ce yawan adadin matasan da su ka yi rajistar neman aikin ya zuwa yanzu, ya nuna azama da farin cikin su na neman samun shiga wannan shirin.

A cewar gwamnatin, shirin zai dauki mutane dubu 400 da za su yi aiki a bangarori da dama da su ka hada da noma da lafiya da koyarwa da gine-gine da kuma fasaha.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *