Asusun bada tallafi na duniya ya tallafa wa gwamnatin tarayya da dala miliyan 890 domin yaki da cututtukan zazzabin cin zon sauro da tarin fuka da kuma cuta mai karya garkuwa jiki.

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce tallafi zai taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiya a Nijeriya, musamman bangaren yaki da cututtukan da su ka yi wa kasar nan katutu.

A watan Janairu na shekara ta 2020, Gwamnatin tarayya ta ce za ta ciwo bashin dala miliyan 890 daga asusun duniya domin dakile yaduwar cututtuka a fadin Nijeriya.

Gwamnatin ta kara da cewa, yaki da zazzabin cizon sauro zai samu dala miliyan 417 daga cikin dudaden, sai cutar HIV AIDS da za ta samu  dala miliyan 329, yayin da cutar tarin fuka za ta samu dala miliyan 143.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *