Gwamnatin tarayya, ta ce ba za ta biya Naira dubu 60 a matsayin kudin sallama ga matasan da su ka ci moriyar shirin N-Power kamar yadda su ka bukata ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wasu daga cikin matasan da su ka ci moriyar shirin su ka gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokoki ta tarayya da ke Abuja.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, matasan sun nemi gwamnati ta biya su kudin sallama naira dubu sittin tare da maida su ma’aikata na dindindin.

Matasan sun kuma ja hankalin gwamnati a kan ministan kula da agaji da ci-gaban al’umma Sadiya Umar Farouq ta sauka daga mukamin ta.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Rhoda Shaku iliya ta fitar, ta ce gwamnati za ta kashe biliyoyin nairori wajen wajen ci-gaba da wanzuwar shirin, yayin da nan gaba za ta sake daukar wani sabon rukuni na matasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *