Gwamnatin jihar Zamfara, ta fara raba raguna dubu 5 da 667, da kuma shanu 993 a matsayin tallafin babbar sallah ga jama’a daban-daban na fadin jihar.

Daraktan yada labarai da wayar da kai na gwamnan jihar Zamfara Yusuf Idris ya bayyana wa manema labarai haka a Gusau, inda ya ce bisa ga al’ada gwamnan jihar Dakta Bello Matawalle ya na cika alkawarin sa na bada kayan tallafi da rage radadi ga jama’ar jihar ne.

Ya ce abin da su ka yi kenan da karamar sallah, inda su ka bada tallafi ga jama’a daban-daban musamman marayu da kuma marasa karfi har dubu 100.

Yusuf Idris, ya ce a wannan lokacin, iyalai da kungiyoyi daban-daban sun samu tallafin kayan abinci da kayan sawa domin shagalin bikin babbar sallah.

Sai dai Kakakin gwamnan bai bayyana ko nawa aka yi amfani da su wajen sayen raguna da shanun ba, amma ya ce wadanda za su amfana sun kasance ma’aikatan gwamnati da kungiyoyi da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *