Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce a yanzu tsaro ya tabbata a titin Abuja zuwa Kaduna, domin rabon da a ce an yi garkuwa da wani a titin Abuja tun watan Oktoba na shekarar da ta gabata.

El-Rufai ya kara da cewa, ganin yadda Korona ke ci-gaba da yaduwa a Nijeriya, dole sai an kiyaye dokar hana yaduwar ta a ko da yaushe.

El-Rufa’I, ya kuma zayyano wasu dokoki da matafiya za su tabbatar da sun kiyaye a lokacin shiga jirgin kasa. Wadanda su ka hada da cewa dole fasinja ya sanya takunkumin fuska a lokacin da ya isa tashar jirgin kuma zai bar shi a fuska har sai ya sauka.

Da ya ke tsokaci game da karin kudin jirgin da hukumar Jiragen kasa ta yi, El-Rufai ya ce shi bai ga wani abin tashin hankali a kai ba, domin shi a wajen shi ma karin ya yi kadan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *