Hadakar kungiyar jam’iyyun siyasa ta Nijeriya CUPP, ta ce tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya fice daga jam’iyyar PDP ne, saboda akwai yiwuwar jam’iyyar APC ta janyo shi ne don ta cimma manufar farfagandar addini a zaben shekara ta 2023.

Kungiyar, ta ce an yi wa Dogara tayin takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam’iyyar APC, ganin cewa shi Kirista ne daga yankin Arewacin Nijeriya.

Mai Magana da yawun kungiyar Ugo-chinyere ta yi wannan bayanin ta bakin mai magana da yawun ta Mista Ikenga Imo.

Ta ce ta na fatan ba a yi amfani da farfagandar fito da Kiristan Arewa a matsayin abokin takarar Bola Tinubu wajen janye Dogara zuwa jam’iyyar APC da wata kila ba za ta kai zuwa zaben shekara ta 2023 ba.

Ugo-chinyere, ta ce game da siyasar Bauchi; gwamnan Bauchi na PDP bai kyauta wa Dogara ba, ya yi watsi da shi duk da cewa shi ne ya yi ruwa da tsaki da kuri’un Tafawa-Balewa a shekara ta 2019.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *