Masarautar Katsina ta dakatar da hawan Babbar Sallah sakamakon matsalar tsaro da kuma cutar korona.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar kuma Sallaman Katsina Alhaji Bello M. IFO ya fitar, ya ce Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman da ‘yan majalisar sa ne su ka yanke shawarar dakatar da hawan Sallar.

Ya ce bisa ga tashe-tashen hankalin da ake samu na ‘yan ta’adda, an umarce shi shaida wa jama’a cewa ba za a samu damar yin hawan Sallah Babba ba.

Alhaji Bello M. IFO, ya ce don haka za su cigaba da yin addu’o’i na samun zaman lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *