Wata mata mai juna biyu tare da ‘ya’yan ta huɗu, su na daga cikin waɗanda su ka rasa rayukan su sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja.

Matar ‘yar shekaru 27 mai suna Habibat Hameed, ta rasu tare da yaran ta da su ka hada da Latifat da Rahamat da Abdulateef da kuma Rabi’u.

Wani maƙwabcin marigayiyar mai suna Israel Musa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:12 na daren Juma’ar da ta gabata, bayan ruwa ya shafe gidajen da ke kusa da wani kogi.

Haka kuma, wasu mutane biyar sun mutu, sakamakon ambaliyar da ruwan saman ya haifar a Suleja da ke Jihar Neja mai maƙwaftaka da Abuja tare da share wasu gidaje.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *