Tsohon shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya sake sauya sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa a kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmed ya wallafa haka a shafin sa na Twitter.

A yau Juma’ar ne, Yakubu Dogara tare da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni su ka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara

A shekara ta 2018 ne, Yakubu Dogara tare da wasu ‘yan majalisa da dama su ka sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *