Gwamnatin Tarayya, ta ce mai yiwuwa ta ce dalibai su rubuta jarabawar GCE a cikin watan Nuwamba, matsawar aka kasa kammala shirye-shiryen rubuta jarabawar WASSCE, ta Afrika ta Yamma cikin lokacin da aka tsaida.

GCE dai jarabawa ce ta daban, wadda ake rubutawa a cikin watan Nuwamba, kuma a fito da sakamakon ta cikin watan Disamba.

Karamin Ministan Ilmi Emeka Nwajuiba ya bayyana haka, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a kan halin da ake ciki game da cutar Coronavirus a Nijeriya.

Minista ya ce canjin ya zama wajibi, ganin cewa babu wani dalilin da zai sa a kara wa’adin lokacin rubuta jarabawar WASSCE.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *