Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wasu manyan Kantuna da Otal-Otal da gidajen cin abinci sakamakon saba dokar Korona,

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne ta ofishin Kwamishinan kasuwanci na jihar Idris Nyam.

An dai rufe gidan cin abinci na Shagalinku da ke kan Titin Ali Akilu, da Cake House da ke Sabon Tasha, da babban shagon saida abinci da buredi na Big Treat, da 7 Stars Restaurant, da fitaccen gidan saida abinci na Baraka, da Aji Nice duk a hanyar Isa Kaita.

Sauran sun hada da Otel din Top Galaxy, da ke Sabon Tasha, da kuma Epitome Hotel da ke Barnawa.

Gwamnatin jihar Kaduna, ta gargadi masu wuraren kasuwanci su tabbatar sun bi dokokin da gwamnati ta shimfida domin dakile yaduwar Korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *