Gwamnatin tarayya ta amince da sabuwar dokar samar da kwalta a cikin gida domin ci gaba da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ministan ayyuka da samar da gidaje Babatunde Fashola ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa.

Ya ce majalisar zartaswa ta tarayya ta cimma matsayar samar da kwaltan a cikin gida ne domin karfafa gwiwar farfado da masana’antu dake fadin kasar nan.

Ministan ya kuma bada tabbacin cewa idan dokar ta fara aiki gadan-gadan za ta taimaka wajen kubutar da miliyoyin kudade da ake kashewa wajen shigo da kwalta.

A cewar Fashola akwai bukatar samar da tan dubu dari biyar na kwalta a cikin gida duk shekara wanda za a rika amfani dashi wajen gyara da kuma samar da sabbin hanyoyi dake fadin kasar nan.  

Ya kuma bukaci bangarori masu zaman kansu a Najeriya da su yi amfani da damar wajen zuba jari a bangarorin samar da kwalta a cikin gida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *