A yau Alhamis shugaban kasa Muhammadu Buhari ke halartar taron tabbatar da zaman lafiya birnin Bamako na kasar Mali, biyo bayan bayanan da ya samu daga jakadan kungiyar rainon tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika Goodluck Jonathan.

Mai ba shugaban kasan shawara han harkokin yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta ce shugaban ya kai ziyarar ce karkashin jagorancin shugaban hadakar kasashen na kungiyar ta ECOWAS, Muhammadou Issoufou, inda suka amince su hadu tare da tattauna mafita kan rikice-rikicen dake da nasaba da siyasa da kasar ke fuskanta.

Sauran wadanda ake sa ran za su halarci taron sun hada da shugaban kasar Senegal, Ibrahim Boubacar Keita, da Nana Akufo-Addo na kasar Ghana, sai Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire.

Wannan na zuwa ne bayan Goodluck Jonathan, tare da shugaban ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou, sun ziyarci shugaba Buhari a ranar Talatar da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *