Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe wasu ma’aikatan hukumomin bada agaji a jihar Borno su biyar, wadanda ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa dasu a watan da ya gabata.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai ba shugaban kasan shawara ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu a Abuja.

Shugaba Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan ma’aikatan agajin biyar da ‘yan ta’addan suka kashe, tare da cewa suna da kyakkyawwar sakayya kan irin gudunmawar da suka gaba a wajen Allah.

Sannan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da cewa an yaki ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban ya kuma jajantawa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno, da sauran kungiyoyin bada agaji da suka rasa ma’aikatansu wajen kai kayayyakin agaji a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *