Hukumar yana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce an samu karin mutane 543 da suka kamu da cutar korona cikin sa’o’i 24, wanda hakan ke nuni da cewa yawan wadanda suka kamu da cutar yanzu ya kai 38,344.

Hukumar wacce ta bayyana haka a shafinta na twitter, ta kara da cewa cutar ta kara kashe mutane takwas da ta kama, wanda yawan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar ya kai dari 8 da 13.

Mutane daga cikin mutanen da suka sake kamuwa da cutar akwai mutane 180 a jihar Legas, jihar da cutar tafi kamari tun bayan bullar ta a Najeriya.

NCDC ta ce masu dauke da cutar ta korona 138 ne suka warke a cikin sa’o’i  24 kuma tuni aka sallame su domin komawa gidajensu domin ci gaba da harkokinsu a cikin jama’a.

Yanzu adadin yawan waɗanda suka warke daga cutar a Najeriya ya kai dubu 15 da dari 815.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *