Masarautar Shinkafi ta ce ba za ta kwance sarautar da ta ba tsohon ministan sufuri Femi Fani-Kayode, ba duk da ajiye sarauta da wasu mutane biyar suka yi a masarautar. 

Wamban Masarautar Sani Abdullahi ya bayyana haka ga manema labarai.  Ya ce nan gaba kadan za a maye gurbin wadanda suka aje mukaman nasu da wasu daban.

Sannan ya yi zargin cewa mutanen biyar na gaban goshin tsohon Gwamnan jihar Abdul’aziz Yari ne. 

Ya ce masarautar ba za ta karbe sarautar da ta ba Femi Kayode ba, saboda Sarkin Shinkafi mutum ne mai kima da daraja.  

Da yake amsa tambaya kan dalilin nada Femi Kayode, ya ce tsohon ministan ya yi nasarori sosai a rayuwa.  

Fami Kayode dai wanda Dan jam’iyyar PDP ne ya yi kaurin suna wajen zagin wasu manyan Arewa, wanda ko ana gaf da nadashi sai da ya caccaki tsohon gwamnan jihar ta Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *