Majalisar zartaswa ta Najeriya ta amince da kashe sama da naira billiyan 10 wajen inganta harkokin hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya.

Minister kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad, ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ta ce an bada kwangilar samar da na’urar gwada kayayyakin da ake shigo dasu akan kudi sama da dala milliyan 18.

Ministar ta ce za a samar da na’urorin ne a tashoshin jiragen ruwa na Onne dake garin Port Harcourt na jihar Rivers, da kuma tashar Tin Can Island dake jihar Legas.

Sannan za a samar da wasu kananan jiragen ruwa guda 10 da jami’an tsaro da na hukumar za su rika amfani dasu wajen zirga-zirga tare da tabbatar da tsaro a iyakokin ruwan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *