Kwamitocin dake da nasaba da lafiya na majalisar wakilan Najeriya sun cimma matsaya kan hada hannu da hukumar lafiya ta duniya WHO wajen inganta cibiyoyin lafiya dake fadin kasar nan.

Kwamitocin sun cimma matsayar ce a lokacin da suka ganawa da sabon jakadan hukumar ta WHO a Najeriya Walter Kazadi Mulombo, a Abuja.

Tun farko dai Mulombo, ya nuna farin cikinsa kan ganawar da ya yi da ‘yan majalisun, a daidai lokacin da yake fara aikinsa a Najeriya.

Ya ce shugabannin kwamitocin da sauran ‘yan majalisun Najeriya sun damu matuka kan hanyoyin da za a bi wajen kara inganta rayuwar al’umma.

Ya kara da cewa hukumar lafiya ta duniya a shirye take wajen hada kai da dukkanin sauran ‘yan majalisu musamman a ofisoshin hukumar dake kasashen Afrika.

A nasa jawabin shugaban kwamitin kula da lafiya a matakin farko na majalisar Yusuf Tanko Sununu, ya ce majalisar ta kulla kyakkyawar alaka da tsohon jakadan kungiyar a Najeriya, kuma za ta ci gaba da dabaka wannan dangantakar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *