Majalisar zartaswa ta Najeriya ta amince da kafa asusun naira billiyan 75, domin bunkasa harkokin matasa milliyan 68 dake da sheka ru ’18 zuwa 35.

Ministan kula da harkokin matasa da wasanni Sunday Dare, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar Dare, za a yi amfani da kudaden ne wajen tallafawa matasa da suka cancanta da dabarun kasuwanci, da kuma hanyoyin da za su rika amfana da basussukan banki.

Ministan ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya ba za ta bari ‘yan siyasa su mamaye shirin ba, domin matasan da suka cika sharuddan da ake bukata ne kawai za su amfana. 

Ya kara da cewa ma’aikatarsa za ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da an bi ka’idoji tare da tabbatar da an saki kudaden da ake bukata domin gudanar da shirin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *