Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ta ce ta kama wasu mutane biyu da ta jima ta na nema bisa zargin su da yi ma wata matar aure fyade sannan su ka kashe ta daga bisani yayin da ta yi yunkurin tona masu asiri.

Lamarin dai ya faru ne a watan Mayu, a wani kauye da ke cikin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Rundunar ta bayyana kama mutanen ne, kwana daya bayan wata nasarar da ta ce ta yi na kama wani mutum mai shekaru 51 da ake zargi da lalata kananan yara mata ciki har da ‘yar shekaru hudu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isa, ya ce za su cigaba da aiki domin ganin an kawo karshen aikata miyagun laifuffuka a jihar Katsina.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *