Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, ya ce ranar Juma’a 31 ga watan Yuli za a gudanar da Idin Babbar Sallar bana.

A wani sako da kwamitin ganin wata karkashin Sarkin ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce sakamakon ganin sabon watan Dhul-Hijjah a wurare da dama ma ranar Talatar da ta gabata, Laraban nan ta kasance daya daga watan Dhul Hijjah.

A cewar sa, an ga sabon watan ne a garuruwan Abuja da Jalingo da Ilorin da Lafiya da Minna da kuma Misau.

Ya ce masarautar Sarkin Musulmi za ta fitar da sanarwa a hukumance da za ta yi cikakken bayani a kan tsarin Babbar Sallah.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *