An ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC da na jamhuriyar Nijar SONIDEP, game da saida wa Nijeriya tataccen mai da za ta riƙa amfani da shi a cikin gida.

Wannan dai ba ita ce yarjejeniya ta farko da kasashen biyu su ka ƙulla a kan lamarin ba, sai dai wannan ne karo na farko da za su ɗauki ƙwararan matakai don ganin yarjejeniyar ta yi nasara.

An dakatar da yarjejeniyar farko ne tun bayan da hukumomin Nijeriya su ka ɗauki matakin rufe iyakokin tudu, lamarin da ya janyo dakatar da shiga da man fetur Nijeriya.

Nijeriya, ta ce sayen man daga Nijar zai rage mata wasu wahalhalu da ta ke fuskanta wajen sayo man da ta ke amfani da shi a cikin gida daga ƙasashen Turai.

Kampanin da ke tace man fetur a jamhuriyar Nijar dai ya  na tace gangunan mai dubu 20 a kowace rana, wanda shi ne za a fara saida wa Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *