Wasu masu rike da sarautun gargajiya 3 sun sake ajiye aiki a masarautar Shinkafi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar masarautar bayan ta nada Femi Fani Kayode sarautar Sadaukin Shinkafi.

Wadanda suka ajiye sarautar sun hada da Bilyaminu Yusuf wanda shine Sardaunan Tsafe, Umar Bala Ajiya wanda a baya shine Dan Majen Shinkafi da kuma Hadiza Abdul’azeez Yari wacce a baya ta rike sarautar Iyar Shinkafi.

Sun ce sun ajiye sarautar su ne saboda abunda ke faruwa a masarautar.

Sun ce bai kamata a ce an ba Fani Kayode sarauta ba saboda siyasa, kamata ya yi duk wanda za a ba sarautar gargajiya ya kasance ya kawo wani ci gaba ga masarauta, ko ci gaba ga yanki, ko ci gaban tattalin arziki, ko samar da tsaro, ba wai a rinka bayar da sarauta saboda siyasa ba.

Sannan sunyi godiya bisa sarautun da aka ba su.

A baya dai Fani Kayode ya yi kaurin suna wajen sukar Arewa da manyan ta, wanda ko a kwanaki ya soki Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *