Gwamnatin jihar Ogun, ta maye gurbin Likitocin da ke yajin aiki dake aikin kula da masu fama da cutar Korona a asibitin Olabisi Onabanjo da likitocin sa-kai.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 1 ga watan Yuli ne Likitocin kungiyar ARD ta fara yajin aiki sakamakon rashin biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi.

Bukatun likitocin kuwa sun hada da rashin sama wa ma’aikatan kiwon lafiya Inshorar lafiya, da rashin biyan ma’aikatan lafiya da sabon tsarin albashin ma’aikata, da rashin isassun ma’aikata  da rashin biyan alawus da sauran su.

Kungiyar Likitocin, ta ce rashin biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi duk da barazanar da ta rika yi na zuwa yajin aiki amma gwamnati ta yi biris da su, ya nuna ba ta shirya neman a yi sulhu ba.

Mai taimaka wa gwamnan jihar ta fuskar yada labarai Olabisi Onabanjo ya tabbatar da haka, inda ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ci-gaba da ayyukan kula da masu fama da cutar covid-19 a asibitin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *