Majalisar Dattawa ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya miƙa mata kasafin shekara ta 2021 nan da watan Satumba, domin samun damar aiwatar da shi a kan lokaci.

Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya na bayyana haka, yayin da ya karɓi buƙatar da Shugaba Buhari ya aika na daftarin hasashen abin da za a kashe a kasafin shekara ta 2021 zuwa 2023.

Bayan karanta wasiƙar da Buhari ya aike masu, Sanata Ahmad Lawan ya umarci kwamitocin majalisar a kan harkokin kuɗi su fara aiki a kan ta.

Rahotanni sun ambato Ahmad Lawan ya na cewa, ya kamata ɓngaren zartarwa ya fara aiki a kan kasafin shekara ta 2021, domin su na so su tabbatar sun karɓi bayanan kasafin a ƙarshen watan Satumba don su duba su amince da shi kafin watan Disamba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *