Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari Kukum-Daji dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna inda suka kashe mutane 24, tare da raunata wasu da dama.

Wani shugaban al’umma a garin ya ce ‘yan ta’addan sun shiga garin ne a kan babura tare da bude wuta kan mai uwa da wabi da misalin karfe 10 na dare a lokacin da ake ci gaba da shagulgulan biki da aka gudanar a ranan.

Ya ce nan take mutane 16 aka kashe, yayin da wasu da dama suka bace jim kadan bayan kai harin.

Ya kara da cewa baya ga wadanda suka mutu an tabbatar da karin wasu 30 da suka jikkata inda nan take aka kai su wani asibiti dake Kafanchan, da St, Gerald da kuma Barau Dikko a Kaduna.

A cewarsa 8 daga cikin wadanda aka garzaya da su asibitocin sun mutu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *