Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar Isma’ila Isa Funtua wanda ya rasu ranar Litinin.
Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da kuma al’ummar Jihar Katsina da ma sauran makusantan marigayin bisa rasuwarsa.
Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin “mutum na kowa da ake matuƙar girmamawa.”

Malam Isma’ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin suna da tasiri a gwamnatin Buhari.

Shugaba Buhari ya ce rasuwarsa ta haifar da babban giɓi ne kasancewar ya taimaka masa musamman a tafiyarsa ta siyasa.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ji ƙan mamacin, ya kuma ba iyalansa haƙurin jure rashinsa.

Sama’ila Isa Funtua ya rasu ne sakamakon bugun zuciya ranar Litinin, a cewar ɗaya daga cikin ‘yan uwansa.
“Mallam ya faɗawa iyalinsa cewa yana son ganin likita amma sai da ya fara zuwa wajen mai aski, sannan kuma ya tuƙa mota zuwa asibiti,” in ji ɗan Uwan nasa.
Kafin rasuwarsa Sama’ila Funtua ya taba rike mukamin minista sannan ya taba jagorantar shugaban Ƙungiyar masu buga jarida ta NPAN na tsawon shekara takwas.
Marigayin ne ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin ƙere-ƙere da ya gina mahimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya.
Alhaji Isma’ila Funtua ne kuma daraktan gudanarwa na farko na jaridar Dimokrat.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *