Babban Hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bukaci ‘yan Najeriya su marawa jami’an soji da sauran hukumomin tsaro hadin gwiwa wajen magance matsalar tsaro a wasu bangarorin Najeriya.

Buratai ya bukaci hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani akan nasarorin da rundunar ke samu a yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Ya ce ba hukumomin tsaro bayanan sirri da suka hada da wuraren da ‘yan ta’adda ke buya da inda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum zai taimaka wajen kawo karshen matsalar.

Ya ce shawo kan irin wadannan matsaloli na tsaro ba abu ne mai sauki ba, amma rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da yin iya bakin kokarin ta na sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Buratai ya kuma yabawa jami’an sojin dake fafutukar tabbatar da tsaro, musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya, da sauran bangarori, sannan ya bada tabbacin cewa nan gaba kadan al’amura za su dawo yanda suke.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *