Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya bukaci al’ummomin Musulmi su fara neman watan Zulhijja a ranar Talata 21 ga watan Yulin nan wacce ta zo daidai da 29 ga watan Zul-Qida shekarar 1441 bayan hijira.

Shugaban kwamitin kula da harkokin Musulunci Sambo Wali Junairu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya bukaci duk wanda Allah Ya say a ga watan a cikin al’umma ya gaggauta tuntubar masarauta mafi kusa dashi, domin tabbatar da an kira an sanarwa Sarkin Musulmi akan lokaci.

Ganin watan na Zulhijja dai a gobe shi zai ba Musulmi damar sanin ranar da babbar Sallah za ta fado, wacce ake yi a kowacce 10 ga watan, bayan gudanar da hawan Arfa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *