Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya ce ba wata barazana da za ta hana majalisar dokoki sauke nauyin da ya rataya a wuyanta an sa ‘yan Najeriya a cikin farin ciki.

Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar sarakunan gargajiya na yankin Oke-Ogun na jihar Oyo.

Tawagar karkashin jagorancin Abdul-Ganiyu da dan majalisa Abdulfatai Buhari ya musu iso, ya ce sun je Abuja ne domin halartar taron jin ra’ayoyi kan kirkiro jami’ar fasaha a garin Oke-Ogun.

Mai magana da yawun tawagar Ahmed Raji, ya ce sun je wajen shugaban majalisar ne domin mika godiyarsu bisa marawa kudurin baya da majalisar ta yi.

Ya ce a cikin sama da makarantun gwamnatin tarayya 30 dake jihar Oyo, ba ko guda da aka kai shiyyar Oke-Ogun, dake da kashi 60 cikin dari na yawan kasan dake jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *